2 Peter 3

1Yanzu, ina rubata maku, kaunatattu, wannan wasika ta biyu domin in tunashe ku, in kuma zuga tunaninku na gaskiya, 2don ku tuna da kalmomin da annabawa tsarkaka suka fada a da, kuma da umurnin Ubangijinmu da mai ceto da aka bayar ta wurin manzaninku.

3Ku san wannan da farko, cewa masu ba’a za su zo a kwanakin karshe. Za su yi ba’a kuma su ci gaba bisa ga sha’awowinsu. 4Za su ce, “Ina alkawarin dawowarsa? Tun lokacin da kakaninmu suka mutu, dukkan abubuwa sun kasance yadda suke, tun farkon halitta.”

5Da gangan suka manta cewa sama da kasa sun kasance daga ruwa, kuma ta wurin ruwa, da dadewa ta wurin umarnin Allah, 6kuma cewa ta wurin wadannan abubuwa duniyar wancan zamani ta halaka, da ambaliyar ruwan tsufana. 7Amma sama da kasa na yanzu, an tanada su domin wuta ta wurin wannan umarnin. An tanada su domin ranar shari’a da halakar marassa ibada.

8Kada ku manta da wanan, kaunatattu, cewa rana daya a gun Allah kamar shekaru dubu ne, kuma shekaru dubu kamar rana daya suke. 9Ubangiji baya jinkiri game da alkawaransa kamar yadda wadansu ke ganin jinkiri. Maimakon haka, yana hakuri da ku. Ba ya so ko dayanku ya hallaka, amma kowanenku ya kai ga tuba.

10Duk da haka, ranar Ubangiji za ta zo kamar barawo. Sammai za su shude da kara mai karfi. Wuta zata kone komai da komai, kuma duniya da dukkan ayyukan da ke cikinta zasu bayyanu.

11Da shike dukkan wadanan abubuwa za a hallaka su haka, wadanne irin mutane yakamata ku zama? Ya kamata kuyi rayuwar tsarki da ta ibada. 12Ku zauna cikin bege da kuma hanzarta zuwan ranar Allah. A ranan nan, za a hallaka sammai da wuta, kuma dukkan komai da komai zai narke cikin zafi mai tsanani. 13Amma bisa ga alkawarinsa, muna jiran sabuwar sama da sabuwar duniya, inda adalci zai kasance.

14Saboda haka, kaunatattu, tun da kuna da begen wadannan abubuwa, ku yi iyakacin kokarinku a same ku marassa tabo da marasa aibu a gabansa, cikin salama. 15Kuma, ku dauki hakurin Ubangiji domin ceto ne, kamar yadda kaunataccen danuwanmu Bulus ya rubuta maku bisa ga hikima da aka ba shi. 16Bulus yayi magana akan wadanan abubuwa cikin dukkan wasikunsa, a ciki akwai abubuwa da suke da wuyar ganewa. Jahilai da mutane marassa natsuwa sukan juya ma’anarsu, kamar yadda suke yi wa sauran nassoshi, don hallakar kansu.

17Saboda haka, kaunatattu, tun da kun san wadannan abubuwa, ku kula da kanku kada a badda ku ta wurin rudun mutanen da ba su bin doka, har ku rasa amincinku. 18Amma ku yi girma a cikin alheri da sanin Ubangijinmu da mai ceto Yesu Almasihu. Bari daukaka ta tabbata a gare shi yanzu da har abada. Amin.

Copyright information for HauULB